27 Faburairu 2020 - 06:08
Sojojin Siriya Sun Kwace Ikon Da Lardin Kafranbel

Rahotanni daga Siriya na cewa sojojin kasar sun samu nasara kwace ikon lardin Kafranbel dake kudancin birnin Idleb.

(ABNA24.com) Ko baya ga lardin na Kafranbel, sojojin sun kuma kwace kyauyuka 18 a yankin, da ya jima karkashin ikon mayakan dake ikirari da sunan jihadi da kuma mayakan sa kai.

A baya bayan dai sojojin gwamnatin ta Siriya na ci gaba da samun galaba a kokarin da su ke na tsarkake yankunan dake arewa maso yammacin kasar daga duk wata barazana.

A kwanakin baya ma sojojin gwamnatin Siriya sun samu nasara kwace mahimman yankuna a yammacin kasar da kuma wasu manyan hanyoyi ciki har da wacce ta hada birnin Aleppo da Damascos babban birnin kasar.


/129